Matar gwamna hausa novel complete

Ad Code

Matar gwamna hausa novel complete

Matar gwamna hausa novel complete


Matar gwamna hausa novel complete

MATAR

GWAMNA

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

United we stand and succeed Our ambition is to entertain  motivate the mind of readers


Written By

 Real Ladingo

Yar mutan Niger


AUZUBILLAHI MINAL SHAIDANIR RAJEEM BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy JanafBismillahir Rahamanir RaheemPage 1Akafta NIGER  Yau ta kama laraba  kasuwar garin wato garin sarki kauyen miryah karamar hukumar damagaram garin cike yake makil da jamaa saboda kasuwar garin yau takeci kuma dama tafi cika da yamma har dare zaka ganta da jamaa maza da mata yan kauyinka nakusa da na nesa abun sai ya baka mamaki ko da yaushe suke watsewa su koma garuruwansu oho da misalin karfe biyar na yamma na hango wata kyakyawar yarinyace yar kimanin 14 year se dai ba fara bace chocolate colour ce doguwa ce saide batada jiki siririya ce kyakywace ajin farko duk da bata ida zama cikakiyar budurwa ba amma masha Allah kominta yayi ba karya saide nan da shekaru biyu zaayi zankadediyar mace agurin duk da tana yar kauye tafe take sam hankalinta ba akwanceba dan satar hanya tai ta sadado jiki ta baro islamiyya saboda ta shiga cin kasuwa gudu gudu sauri sauri take tana rumgume da wani katon Allo Wanda yakusa rabin tsayintadon tasan indai malam shehu yasa aka kamota baayi fatiha ba to sai ya mata bulala goma saida tayi nisa ta fara tayifa cikin nutsuwa tafe take tana waka cikin zazzakar muryata saini Fatima zahara matar gwamna idan Allah ya yarda wani katon kara ta gani ta sunkuya ta dauka  bari na dauka saboda tsaro


Tafe take cikin dan kauyasu da bai fiye girmaba tana wakarta da katon karanta ahannu da da dirkeken Allonta Wanda babu yada baayi tarabu dashiba ta dauki Quraan don yanzu kaf kauyen garin sarki sai kace watisme matar gwamna mai Alllo shine cikeken sunanta agarin wani dan lungu tabi dan tayi Saurin isa gida ai ko taci karo da Nawalu mai goro andau wanka cin kasuwa da tiransa na goro akai idan kaga damara da yayi abun dariya yana washe baki ah watutuna daga ina kuma zolayace yasan daga islamiyya take tunda ga dirkeken Allonta arumgume kai na dauke na hade face dan ko kallonsa nayi tashin zuciya nakeyi dan Nawalu kazamine na bugawa ajarida na ci gaba da tafiya amma dan tsokana sai cewa yayi  watutuna Allah ya kaimu ranar auremun Aradun Allah duk makadan kauyukanmu sai an agaiyacesu ya fada yana washe bakinsa 


Da yayi jawur da goro fuska ta kwakwabe ta zubar da yawu  wlh Nawalu Allah ya isa ban yafema ba banza kazami Abbana ba ya rabani da kaiba  yanzu zan turo iyayena su kawo kashe gidanku katon banza mai warin jaba  matar gwamna kakema iskanci wlh sai na fadawa Aunty Malika idan ta kirawo Abbana kasan ai mijinta Attajirine Alquraan sai ya hadaka da hukuma akai ka binni can damagaram adaure ka mai tsamin baki kawai ya daga baki zaiyi magana kafin yayi magana ta gyara Allonta ta kwada masa karan hannuta saida tiran goron ya juye akasa ta zunduma da gudu  kuma gobe kamun magana haka zanma tunda bakada zuciya ta karya kwana da gudu baki ya ciza na kamaki hegiya mai dauda in ba niba ma wa zai soki ya tsugunna yana kwashe goronsa sai tsine  mata yakeyi acikin ransa


Tunda ta fara gudu bata tsayaba sai asoron gidansu yau na mata magana ko kallo bai ishetaba ta tsaya tana maida numfashi tayi dam ta leka iyayye bata tsakar gida buta ta dauka ta debi ruwa a randa ta shiga bandaki ta watsa ruwa ko sabulu bata goga ba agagauce ta fito tashiga daki ta cacaba kwalliya Jan baki har kusan haba jagira baa maganar dabak dabak tayi ta saka dinkinta na sallah ta fito tana leke iyayye bata gidan aranta tace yanzu haka tana gidan haja nanu to na fasa zuwa ma ta bani nacin kasuwa salon iyayye ta hanani  wuff ta fita daga gidan akofar gidansu taga yau da tiredarsa dan shi yafi jin dadin zama ana saboda yan cin kasuwa wasu hanyar suce nan yana samun kasuwa sosai tunba masu shan sigari ba kallonsa tayi


Taga hankalinsa gurin ba wani canji ta warci halewa ta zunduma da gudu tacekayi lisafi gwamna na zuwa zaa biyaka ta tafiyarta sai yanga takeyi baki ya ciza zakici gidanku Maras kunya wani gwamna zai dauki mahaukaciya saide mai faskare  itako gidansu kursu ta ma tsinke itama ta gama shiri ta shigo da sallama kursu tace watsime Aradu da natafi ke ranar kasuwa wayake zuwa makarantar Allo hararata tayi  mutafi dai ai kinsan baa barina naci kasuwa idan ban jeba islamiyya yanzu ma gudowa nayi kuma wlh idan baki fasa fadin sunanan ba Aradu sai namiki dukan mutuwa kema kin fara zama yar bakin cikin matar gwamna idan kin fada me zai rageki irin kune ko kunje gidan wlh zan hana kar abarku kushiga saboda baku cancanci zuwaba saboda kwarmato zai kaiku  to yi hakuri kawata muje Nice fa babbar kawar Amarya 


Wai gwamna na ina kikeso baki ta turoko na inama ko na Saudia ko Niger kasata ko wani gari a niger ko  Nigeria a ko wane gari a Nigeria ko Mali ke ko na London ne na samu nayi manage dariya kursiya tayimudai muna kauyan damagaram ba ruwanmu da daukar dala ba ganmo tsaki tayi aikin banza kijira ki gani zan daukeki yar wanke wanke suna tafiya sai turo baki take suna shiga kasuwa jamaa aka fara sai matar gwamna mai Allo bakinta yaki rufuwa kursiya tace wlh mahaukaciya suka daukeki cikin masifa tace eh sunfi ki tunda suna fadin son raina kefa yar  Allah ya baki hakuri muje daide zasu wuce 


gunri masu kifi lado mai kifi da tiran kifinsa a kai ya taresu yana washe baki watsime zo ga kifinki da kudi dalarki arbain tacin kasuwa fuska ta yamutsa ta matsa da baya ta rike kugunta tana kallon ican rumfar da take kusanta bakinta sharaf janbakin ya fara bata mata fuska budar bakinta sai cemasa tayi  lado wlh kajira ka gani tun kafin mukoma ga mahaliccinmu zaimun sakaiya akan ka wlh kai ko bakada zuciya maye kawai ina koraka kana bina yo ko maza sun kare mezan dakai ajinka kaja raayina da wani shegen kifi da kudi ganin abinda take shirin aikatawa kursiya ta jata suka bar gurin shiko lado ko ajikinsa dan ya saba da tijara watsime sai baki yake washewa yana binta da mayan kallo 


 watsimena in Allah ya yada ke din matace zaki rika farfesun kifi kina morewa agidana yan gurin abokan sanaarsa dariya suke masa dan sunsa borin kunya yakeyi tafiya yayi ya bar musu gurin itako suna can ana yawon kasuwa tacika tayi fam saboda lado ya bata mata rai gun kawarsu suka tafi sailuba   mai kosai cikin saa ta sayar suka shiga yawo kai watsime akwai farin jini duk inda tayi ita samarin kauye kema caa itako ko ajikinta su kursu sunyi sunyi ta musu wayo taci kudinsu kamar yada sukewa samarinsu takiya sai gurin Abbanta taje yabasu kudin cin kasuwa sai da ana Kiran magrib suka bar kasuwa akofar gidansu watsime 


sukayi sallama ta fada gidan da sallama lokacin iyayye na sallah buta ta dauka ta shiga bandaki ta fito tayi alwalla ta shiga dan dakinta tayi sallah koda ta gama tajima tana Addua dan yarinyar akwai addini sosai duk da karalcin shekarunta tana gamawa ta fito iyayye ta kalleta wlh Zahara zakici gidanku ai na biya ta makarantarku akace kin gudo baayi fatiha ba jikinta ta fada tana kukan


 sangarta haba iyayye ta dududu mintina nawane sukayi saura kiyi hakuri uwata kinji Dole iyayye ta dara  to naji amma kibari kina amsar fatiha a makaranta  to naji iyayye Abbana bai shigoba ne  yana masallaci Albishirinki goro   Malika suna tafe ranar Jumaa jibi Kenan kuma sun nemi Alfarama zasu tafi dake Gombe mijinta yace zai rikeki Amana kinsan ba zama yake agariba yana wajan aiki sai karshen wata yake zuwa to kinsan Malika da sakwarta gashi ba wani yaraba gareta masu wayo ba gashi anma kanwarsa aure satin da ya wuce dama itace agurinta shine ta tada masa hankali ya roki Abbanki Alfarama abasu ke zasu saki secondary School can tunfa haihuwar yan biyu da tazo taso ta tafi dake to kiriniyarki ce nake dubawa shiyasa na hanata to yanzu Abbanki yasa baki Dole na yarda ihuu watsime ta saki cikin farin cikin ta rumgume mahaifiyarta  iyayye na gode wlh dama bayau nakeson komawaba tun zuwan da mukayi kaita duk da ina karama yanzu shakara hudu lokacin ina da shekara goma amma naji dadin garin sosai iyayye yanzu acan zanyi makarantar in Allah 


Ya yarda ki tsaya kiyi karatu ki cika gurin mahaifinki don Allah kicire haukan da ke kanki yanzu garinan sun daukeki mahaukaciya wai matar gwamna wani gwamna ne zai auri yar kauye kuma talaka futik fatima zahara ina miki fatan Alkhairi Allah ya albarkaci rayuwarki kamar yada ya Albarkaci rayuwar Malika kizamo mai nutsuwa kibar shirme kinji  to iyayye naji kawai dama dan ayi dariyane nakeyi amma nafasa kinji yauwa Allah miki Albarka Ameen Abbane ya shigo da sallama zahara ta Mike da gudu ta taresa ta ruko hannusa Ah mama ina tsarabata ta kasuwa  dariya tayi Abbana mun cinye fah zama sukayi iyayye tayi masa sannu da zuwa  Aisha ya gida  Alhmdllh Abban Malika ya kasuwa  Alhmdllh  to bari muyi sallah sallahr 


Isha sukayi ita da zahara iyayye ta zubo musu tuwan dawar masara da miyar kuka taji daudawa da man shanu Abba ya basu ledar balangun da ya kawo sukaci tuwansu cikin jin dadi da annashuwa dan duk shirmen watsime bata taba rena gidansu ba da abincinsu kuma duk haukan da maza keyi bisa kanta da kudi da kayan ciye ciye da suke bata har yau bata taba amsaba dan ita yarinyace da abun wani bai taba burgetaba ta dogara da gidansu da iyayanta bayan sun gama ta kwashe kayan ta kaisu madafa ta wanke hannuta ta dawo kusan Abbanta ta zauna tana washe baki mama kinji zaki Gombe zakiyi rayuwa da yar uwarki zasu saki makaranta wlh da sam ban aminceba to kinsan yada muke da mahaifin yaron yama mahaifinsa magana yasa baki shi ba mazauni bane gashi hafsat da take gunsu anyi mata aure dama itace karamar da ta rage acan gun iyayansa to sunce zasu rikeki Amana to dan Allah ki nutsu karki rika shirmen da kikeyi 


Wai ke matar gwamna anaso a maidamun yarinya mahaukaciya agari wlh abun na damuna wai sai kace watsime matar gwamna mai Allo yo ina dan dalili wlh abun na damu har cikin dare nake tashi ina sallah Allah ya rabaki da wannan shirmen dan shirmene wani gwamna zai kwashi yar kauye koda kin girmama bare dudu yanzu kikeda shekara sha hudu dan Allah ki cire wannan shirmen kinga babban birni zaki wlh sa koroki baa musu shiririta ki kasance tamkar yar uwarki ina miki fatan Alkhairi Allah ya baki Abunda kikeso na kirki ba shirmeba Wanda hankali ma bazai daukaba Abbana nagode insha Allahu nabar shirme karatu zan tsaya nayi Allah miki Albarka dariya Aisha tayi


 to Allah yasa nima tace ta bari  Allah nabari ni duk Wanda ma yace matar gwamna sai munyi fada dashi sosai iyayan nata sunji dadi suna kara dorata a akan hanya  dan sunsan abin da take ba daide bane sun jima suna hira sai da dare yayi sosai ta tashi ta shiga dakinta tayi shirin kwanciya da kudirin babu wani zancen gwamna aranta tayi kwanciyata har bacci ya kwashetaNigeria Gombe  Federal lomcost misalin karfe 12pm Na dare wani hadadan gida tamkamemansa kana ganinsa kasan mai shi nera ta zauna kaina na kutsa cikin wani hadadan parlo Wanda ya gaji da haduwa yaji kayan Alatu wasu lumtsuma lumtsuman kujeru ne a parlon har kala biyu wata makekiyar Tv na gani wacce takusa cin rabin bangon da yake manne da wani daki parlon shiru ba kowa amma Tv a kunne wannan dakin mai manne da tv na shi saida nakusa sumewa saboda wani mayan kamshin dadi da yadaki hancina ga kamshin Ac wani Royal bed ne yaci kusan rabin dakin ga wasu kujeru manya manya capet malala ko ina ashimfide kallona nakai don naga waye akwance 


Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan bawan nashi gashide magidancine zai kai kimanin 48 year amma jin dadi da nera sun samu zama jikinsa zaka zaci bai fi 40 year ba iya karshen haduwar namiji wannan mutum yakai idanusa lumshe yake yayi daidai dagashi sai gajeren wando fari tas dogo mai cikar zati gashin kansa luf luf sai sheki yake yanada dogon hanci da manya idanu kirjinsa cike yake da gashi yanada kirar karfafa saide fa miskine na karshe fuskarsa ta kawatu da saja gemunsa mai mutikar kyawu ya karamasa kyawun fuska wata kyakyawar mata fara tas yar duma duma mai matsagaicin tsayi ta shigo da sallama yar kimanin 31 year  saman bed din ta hayo ta dora kanta kirjinshi tana shafa fuskarsa my man kayi bacci ne idanusa ya bude saboda bacci yake amma tana tabashi ya tashi yana mamakin mafarkin da ya tisasa gaba na hasken tauraruwa mai tsananin haske ta fito tana cewa ranar da zan baiyana kasarka ranar zakaci zabe duk da bakaso amma Dole sai kaci saboda talakawa na sonka kuma nima ina sonka kaidin rayuwatane karka dubi kaskantata ba ruwan Allah idan yaso ya hada Abu to hikimarsa ce kuma shi yanada dalilinsa nayin hakan don haka ka taimaki na kasa dakai kaji tausayin na kasa dakai ka kasance mai yawan sadaka yana jin dadin zazzakar muryata hasken tauraruwar sai ya rika mamaki tauraruwa bama mutumba amma Takeda wannan dadin murya haka tunanin ta katse masa  my man lumsassun idanuwansa


ya zuba mata ya daga mata gira murmushi tai masa janyota ya rungumeta suna kallon juna har ta sa aranta tace yau fah ko zan kwana ina magana ba laleba ya amsamun cikin saa taji amon zazzakar muryasa yana mata magana tamkar bayaso yana cewa sahibata tauraruwar zuciyata my bintuna mijinki na bacci kika tasheshi ina yarana da baby Rauda shagwabewa tayi tana shafa fuskarsa tayi bacci ita kamar yarinya mai shan nono shakara biyar amma idan ba ajikina ba take bazatayi bacci ba shine nazo na ganka dan nasan yanzu haka tunani ya dameka tunda naga ka killace kan kai daya my man jibi muna sa ran nasara kiss ya mata saman lips dinta ya tsareta da lumsassun idanusa cike da tsananin kaunarta yanaji aransa bazai iya taba son wata maceba kai ta langwabe tana lumashe idanuta dan yada yake mata wani shegen kallo ya sakar mata kasala  my man gira ya daga mata ya saki dan guntun murmushi bai sake maganaba tun tambayar da yayi mata ya fara shafarta yana sakar mata kiss a cikin kunneta ya fara rikirkitata da salonsa mai tafiya da zuciyarta Wanda ta yarda mijinta ita dayace agabansa ta sani ba yau ba my man dinta baya gani ko wacce mace sai ita ita dayace acikin zuciyarsa yan zunma ta kara tabbatarwa yada yake kallon lips dinta ta gane kissing dinta yake son yi bakinsu ta hade dan ta yada da mijin nata mai tsada ne mata basa gabansa duk da mata na kawo masa hari basa gabansa sai ita daya shiyasa miskilancinsa da rashin son maganar sa baya damunta don ajininsa yake babu abinda zai canza shi tunda ta kasa hakan duk kuwa zazzafar kaunar da sukewa junansu sun jima sosai suna farantawa junansu rai cike da tsantsar 


Kaunar junansu basu yi komaiba bakinsu romance sai karfe biyu suka hakura da tande tande da lashe lashen juna ya lallabata har tayi bacci ya janyeta jikinsa ya rankwafa ya mata kiss akumatunta cike da tsantsar kaunarta mikewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito daur da towel ya dauki jallabiyar da take saman dadduma yasaka tana wani fitinanan kamshi zuciyarsa na mamakin wannan mafarki sallah ya tayar kamar kullum  ta neman zabin Allah kan wannan shugabanci da yake tunkaroshi dan hasken tauraruwar na kara jadada masa tabbas sai yaci zabe to abin da yake damunsa da take cemasa tana dirowa kasar sa zaici zabe shine ke damunsa shiyasa ya dage da Sallah d Addua
bayan kwana biyu tun da iyayanta sukayi mata fada ta shiga hankalinta ta cire maganar gwamna aranta ko kace mata ta gwamna to zatace bataso idan kaki saide kaji ta zambace ta rafka maka wani Abu ta gudu to ganin haka yasa aka fasa fada mata agabanta cikin kwana biyu kacal don sunsa ita ta jiyataka babu ruwanta ta ajiye katon Allonta da Quraan take zuwa islamiyya abun yama iyayanta dadi sosai da misalin karfe biyar da rabi na yamma tafe suke ita da kursu sun fito daga gidansu kursun zata rakata gidansu tace suke suna hirasu cikin wasa da dariya sunci uwar kwalliya fuska yababa da hoda da Jan baki da katon karanta ahannu saboda tsaro duk uban da yace mata matar gwamna taci ubansa dan yanzu tafi son karatu akan wani gwamna da 


 Ba samu za tayibaniko nace haba Teemah ai cama ma da rikici sai munje Gombe sun biyo wata yar kwana dede kofar gidansu Nawalu mai goro yana zaune da tiransa ya washe baki  watutuna barka da yamma dariya kursu  ah Nawalu ya garin  wlh kursiya lahiya nake keda gimbiyata Jan kursu tayi da karfi suka bar gurin tana masifa wlh bakida hankalin da kike biyashi dariya tayi suka tafi yabisu da kallo  hegiya watutuna wlh idan ta kara warwarewa akwai kayan aiki ya fada yana lasar baki suko suna karya kwanar gidansu watsime su kaga daleliyar mota ihu ta kurma ta saki hannu kursu ta fada gidan da gudu kursu ko tsaye tayi tana kallon motar mai shegen kyau yara suna kewaye da ita sai washe baki sokeyi suna cewa Alquraan minjin maleku yazo da mota mai ruwan jirgin sama kursu tace musu  dallah can kauyawa banza wannan ai tafi ruwa da jirgin kasa gidan ta shiga da gudu bata tsaya taji mai zasu ceba yau mai tireda sai washe baki yakeyi dan yau sai ya fida kunyasa ya roki 


ya samome ko da goge goge da wankine ya koma birni watsime na zuwa ta fada jikin Malika tana dariya  wlh addata naji dadi sosai da zuwanku yan biyu ta kalla kimanin yan 2 year da sauri ta rusuna  Yayana ina yini sannu da zuwa ya hanya dariya muazam yayi  Alhmdllh fatima iayayye tace  wlh kedai anyi sakara saida kika idar da surutun zaki gaishesa yaran ta dauki daya  kai Shuriem ykk fuska ya kwakwabe zaiyi kuka saukesa tayi dan dama yara ba wani damunta sukayi ba ta nufi gun Rasheed shima kiyawa yayi muazam yacekiyi hakuri zasu saba dake kuda zaku zauna gu daya Malika tace gajan hakuri wa zai mata kursu ta shigo tana washe baki tana gaishesu dariya ce ta kama muazam ganin yada fuskarsu tayi yaba yaba da kwalliya kursu ta nufi gun yaran suka saka kuka suka nufi gun uban su iyayye tace kai kuma da kwawa kuke ai bazasu yadaba jifa yada kamarku take fuska kamar sabon shiga dariya sukayi suka koma gefe suna kallon Malika da muazam dan yanada kyau sosai   sam bazaka taba cewa Malika daga kauyen garin sarki  aka auretaba ba hira suke cikin jin dadi da annushuwa kasancewar muazam mutum ne mai bar kwanci shirmen da watsime takeyi da ita da kursu yana sakashi nishadi shi dama bashi kyamar mutum sam saboda shima garin mahaifar iyayansa ce kaddara ce ta fitar dasu sai dab da magrib ya fita domin zuwa masallaci suma mikewa sukayi kowa yayi shirin sallah kursu sai bayan sallah magrib watsime ta rakata da jadada mata gobe ta kaimata tsarabarta bayan sallah isha suka shigo da Abba iyayye ta zuba musu girkin da tayi musu zabbi ne har biyu manya manya anata Na kiwo ta yanka sosai muazam yaci saboda dafuwar tayi masa dadi sosai dama inda sabo ya saba da girkinta akwai dadi su Malika ma sunci sunyi kit ita da yaranta sai santi suke watisme na dariya Malika tace zahara kin iya irin girkin iyayyemu  Aunty na iya fah  to ai zan koya miki ko baki iyaba su Abba dariya suke musu haka sukayi ta hirasu Abba da kansa ya gyarawa muazam inda zai kwanta 


dan agajiye yake haka yayi musu sallama yaje ya kwanta cikin ikon Allah duk da babu wuta an bude masa taga iska na shigowa hakade ya daur yana fifita yo abunka da Wanda ya saba kwanan Ac  suko hira suka kusa kwana sukayi suna hira har barawon bacci ya kwashesu Asubah ta gariyau ta kama lahadi kuma yau zasu tafi tun safe watsime bata zaunaba suna bin yawon yan uwa ita da Malika ana ban kwana dama daukantane sukazo ba saboda gobe da yamma zai bi jirgi ya tafi Lagos gun aiki sai kusan shabiyu suka fito daga gidan haja nanu kakarsu mahaifiyar Abba watsime sai kuka takeyi dan ta saba da ita bacci kadai ke rabasu da kakarta gashi yau zata barta kursu ma kuka takeyi ko da sukazo basu zaunaba Adadafe suka shirya kayansu dan Ana sallah Azuhur zasu dau hanya iyayye sai lallaba su take suyi hakuri ai basu rabuba da zaran ta samu hutu zata rinka zuwa to da hakane kursu ta daina kukan bayan sallahr Azuhur muazam yace su fito ya ba Abba kudi ba kadan da iyayye kamar yada yaje rabama daidai kun yan uwansa dama ya kawowa su iyayye kayan abunci duk abinda zasu bukata 


suna fitowa kofar gida jamaa caa lado sai hawaye yake yana tsaye dan Allah yana gani baiso tafiyarba Nawalu sai harara lado yake yana Jan tsaki ya toshe hanci  dallah malam bar nan mu ba karnin kifi muke son jiba ko kallonsa lado baiba Abba ya kallesu ya girgiza kai dan Allah yana gani acikinsu ba Wanda zaiba yarsa sai yasamu nutsatse mutum itako gimbiyar ko kallo basu ishetaba ta rungume iyayye tana kuka daket ta lallasheta tayi shiru ko me ta gaya mata har ta fara dariya kursu na rike da ita har bakin mota Malika ta rungume mahaifiyarta tana hawaye saida ta lallabata suka shiga mota su Malika suna GABA ita da muazam iyayye da kanta tasa zahara a mota Abba daurewa kawai yake Allah yana gani bayason yarsa tayi nisa dashi bare ba jin magana takeyi ba duk da yaga kwana biyu ta nutsu dukowa yayi yana mata magana kome yake cemata sai kai take dagawa cike da nutsuwa su muazam ko dariya suke kasa kasa don sunajin abunda yake gaya mata motar ya rufe jamaa sai hannu suke daga musu kawayanta na tsaye dayake kaf dinsu da kursu suke shiri dan tare sukayi karatunsu na primary School dinsu har suka gama yanzu shekara daya Kenan dan kauyan babu secondary school sai can miryah ko damagaram ana shirye shiryan ta shigane wannan tafiyar tazo to gashi ita zata tashiga secondary school suna tsaye har motar ta daga iyayye harda hawayenta dan de kawai tanaso yarta tayi karatune Abba ya bi bayanta dan ya lallasheta mutanen gurin kowa ya kama gabansa kursu aka nufi gida ana hawaye yau ko baki yaki rufuwa dan yaji dadin tafiyarta duk tabi ta cinye masa kayan tireda yaji dadin yada muazam yace yabashi lokaci zai nemesa motar ya harba kan titi sosai yake tuki cikin nutsuwa da kwarewa suna hirasu da Malika kida na tashi cikin motar dan tsoka sai ya beko hannu yana tsinkon Malika yana murmushi sanin halinsa na tsokana taki biye masa tace kaji dashi gira ya daga mata yana dariya ya maida hankalinsa kan driving yaran kuwa sun sake da Watsime itako sai kallon yada ake gudu da mota takeyi  kafin mintina arbain har sun shigo damagaram su watsime sai zazaro idanu akeyi anga babban birni dan rabonta da garin tun da ta dawo daga Gombe kusan shekara hudu basu ko tsayaba sai Unwala Stores da tafi ya jido musu kayan tande tande ya basu habawa su watsime sai idanu ake zarewa chocolate sukaci da yara iya cinsu da da biskit da ice cream sai ihu take sanyi amma taki daina sha muazam dariya kawai yake har burki yakusa kwace masa don shirman Watsime nasakashi nishadi saida Malika ta rungumosa tamasa rada akunne ya kaimata dukan wasa suka bushe da dariya ya dauki hanyar Kano wanwait watsime anci anyi nat sai zaro idanu akeyi ga sanyi Ac na mota na ratsata habawa sai barci harda salebartaAkwai kafce fah agombe

 amma duk da haka sai naga karbuwarsa gun jamaa zan ci gaba idan ya muku zanga sakon kudon haka ina so naga 

karbuwar Matar Gwamna

              

22796515805


insha Allahu zaku rika samun posting sau ukku a sati asabar da litini da alhamis Amma sai naga kalar karbuwar Matar gwamna don inada nasiyarwa gabana idan najiku shiru Aradu sai na aje na koma gefe na Kafta wasan ZEE BABY HATSABIBIYA RAMLAT RETURN  amma fah nasiyar wane

Rahma ce Ummu FareeesaMATAR

GWAMNA
    ___________________________________KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

United we stand and succeedOur ambition is to entertain  motivate the mind of readers

httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation

___________________________________


Written By

 Real Ladingo

Yar mutan NigerUwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy JanafAgaskiya bansan yada zan kamanta godiyata ga masoyan matar gwamna ba wallahi ban taba tunanin zaku karbeshi hakaba Aradu saida nace Ashe dama bansaka number naba amma karku damu Ladingo nagodiya da yada  kuke kaunar matar gwamna saidai ina neman Afuwarku korafinku bai karbuba na nadinga yimuku posting kullum hakan bazai samuba abubuwa sunyimun yawa gashi ina book na kudi mu de barshi so ukkun asatin amma kusani Real Ladingo nayinku over kamar yada kukeyin matar gwamna ilove you mazga mazga gunduma gunduma tafka tafka kuji dadinku masoyan matar gwamna


Bismillahir Rahamanir RaheemPage 3idanunsa ya zaro yana cike da mamkin me mahaukaciyanan take shirin masa sai sharbar kaku takeyi idanusu ya sarke guri guda zuciyoyinsu suka buga atare  wallahi bazan yadaba akanme zakace mun mahukaciya mekagani na hauka jikina kawai Dan Allah ya jarabeni da sonka tun ban sankaba to bari na nunama haukan ta fadi tana kuka tana dab da cinmasa sojoji sama da mutum biyar sukayi kanta daya ya saita bindiga zai harba mata Mai girma governor ya daka musu tsawa don muryar Noor dinsa gareta gashi irinsu masu tarin makiya abin yayatawa aduniya irinsu bayada wuya cikin basar da shirman yarinyar yace  maza ku dauketa akaita asibiti abata kulawa ta musamman zanzo har hospital din domin duba sauran mahaukata yan uwanta ya fice gurin taron Wanda yake cikeda jamaa Wanda Sam hankalinsu bai bado abinda yake faruwaba Maheeda kuka ta fara ganin wani murdedan soja ya dauketa yasakata cikin wata mota ta nufo gun tana kuka amma kafin ta iso motar ta fice daga cikin makarantar da taso taje gun taron tayi bayani tsoro ya hanata baya ta tsaya tana kallon yada ake girmama gwamna da yada ake karamashi kyau tutukan da yakawoma daliba ya bayar da kudade masu yawa har cikin aji aji yarika shiga na manya 


da yara barin gurin nayi na bi bayansu watsime babbar hospital din gombe suka nufa da ita sai ihu take tana kukan takaici wannan sojan da ke tare da ita wata irin tsawa ya buga mata wacce fitsari ya kusa zubo mata babu shiri tayi shiru jikinta na rawa har suka iso hospital din yana rike da bindinga sai idanu yake zarowa ya buga mata tsawa ta fito tana gaba yana binta suka shiga har cikin reception suna shiga nurse biyu suka taresu don har ga Allah sun zata batada hankali magana yai musu dayar atsorace take haka suka damketa akayi bangaran mahaukata da ita sai kuka take dayar tace insha Allah wannan da wuri zata warke tunda tana kuka yarinya kyakywa gani sun kaita wani daki da wasu irin naurori yasa hamklinta tashi sai ga doctor yashigo da wata zungureriyar Allura ahannusa tace  Dan Allah kumun rai narantse muku da Allah inada hankali ni ba mahaukaciya bace kwalliyar garinmu nayi idanu Dr ya zuba Mata yana karanta yanayin yarinyar tabbas da hankalin OK idan ba mahaukaciyaba mai ya kaiki tunkara governor da rana kai tsaka wlh yanzu da ankasheki abanza dan kinci saarsa adalin mutumne baya saukin yanke hukunci sai yayi bincike kuka take wiwi tana Kara nadamar sanin wani gwamna arayuwarta


matsowa yayi zai mata Allura ta shiga magiya kar ya mata gwaje gwaje ya fara mata kusan awa biyu ya tabbatar lafiyarta lau zama yayi kusanta  inaso ki fadamun tsakaninki da Allah waye ya turaki gun gwamna idan kin fadamun gaskiya zan barki ki tafiyarki lfy idan kin fadi akasin haka to fah zakiyi ta rayuwa gidan mahaukatane to zabi ya rage naki cikin Kara nadama tana kuka tace bama gaskiyar sa kadaiba harda asalina zan fadama kuma daga yau ko shine autan maza wallahi Allah na cireshi araina da farko ni sunana Fatima zahara ni haifafiya garin sarki wacce take kauyan damagaram a niger mahaifina sunansa Muhammad Bashar Dan dinga mahaifiyata sunanta Aisha Abubakar bafilatanace ta asali gaba da baya daga ita har shi haifafun rugane kauyan gidimouni auran gidane akayi musu da banana Wanda bayan auran da shekara ukku suka bar rigage suka 


Dawo garin sarki da zama Abbana kantine gareshi yana sayar da kayan masarufi anan Allah ya basu  haihuwar da namiji amma baizo da raiba sai bayan shekaru biyu aka haifi yayata Malika wacce ta sami gata da tarbiyya Dan zuwa lokacin iyayan babana suma sun dawa garin sarki tunda bamuda wani Dan uwa abinni bayan haihuwar yayata saida aka shekara bakwai tukun aka haifeni Wanda naji jamaa na yaba kyawun da Allah yayimun duk ni ba fara baceba inada kyau duk da mu talakawane amma iyayanmu basu ragemu da komaiba daga kaina har yau Allah bai sake ba iyayamu haihuwa ba muntaso nida yar uwata cikin gata da kulawa gun iyayanmu da kakanunmu kamar su lashemu munsu tarbiyya daide gwargwado agaskia tun ina yar karamata banaji magana akwai dauke dauken magana Dan nafasawa mutum kai da dutse ni ba wani Abu bane agurina haja kawai tun da na fara tasawa na lagabawa kaina suna da matar gwamna bansan wani gwamna ba haka sai kaiwa naji inason sunan ko gobe kaje garin sarki sai kace watsime matar gwamna mail Allo cikin ikon Allah muna dab da zuwa gombe iyayane yawan nasiyar da suka mun Dan sunsa abin ba mai yuwabaneba har na hakura na bar maganar cikin raina yayata tayi karatunta har ta gama secondary school acikin garin damagaram Allah ya hadata da mijin da take aure yanzu mutumin nan gombe ne sun hadune gun auren kawarsu kuma shima iyayansa haifafun garin sarki  kaddara haihuwarsuce ta maidosu nan gombe da kuma rabon arzikinsu acan sunyi aure cikin so da kaunar juna shekaru


 hudu da suka huce ni nayi primary 1 zuwa primary 6 agarin sarki yanzu shekara daya da na gama mijin yayata ne ya tsayami ya madoni gombe yanzu a SS 1 nake nan ta bashi labarin abinda yasa ta Mari maheeda da abinda gomna ya cemata har ta bishi da yada take sonsa tsakaninta da Allah 


Mamaki me ya cika Dr yakebinta da kallo zufa ta karyo masa Dan yasan  ta dauki dala ba ganmo  to agaskiya nasiyar da zan miki ki cire shi aranki Dan ba tsaran kibane kuma abinda kikayi yau kasada ce kikayi da an harbeki fah kuma ba komai ya janyo miki wannan sai kwalliyar hauka da kikeyi to ya kamata kinutso ki waye kinfa fara zama budurwa shekara sha hudu nasiya yai mata sosai tayi masa Alkawalin ba ita ba gomna ta rabu dashi har abadan tare suka fito ya bata dubu daya yace ta hau abin hawa amma fur taki amsa yayi yai takiya daket ta yada ya dauketa amota ya kaita har kofar get din gidansu tayi ta masa godiya yaja ya tafi ta shiga gida ko sallama babu ta fado parlon kamar anjehota 


Malika na zaune tana waya ta ganta kan kujera ta fada ta fashe da kuka Dan abin yana mata ciwo gashi duk da karamcin shekarunta tana jin son gwamna da ta hada idanu dashi ga muryasa ma dadin gaske lokacin da taji na maganar karsu kuskaura su tabata Malika ta kalleta  Teemah lafiya ina jakar makarntarki tashi tayi cikin shashekar kuka tazo ta rungume malika ta labarta mata duk abinda ya faru hankalin malika yayi mugun tashi mutuka ta rungume el uwata suna kuka tare ba mai lallashin wani saida sukaga shuriem da Rasheed sun fara kuka suka gyale malika tayi ta lallashinta Akan ta fita sabgar gwamna ba santabane kar aje kasheta danma adaline yanada tausayi da wanine yana kallo zaa kasheki abanza Dan Allah ki nutsu Ashe duk


Yada na hanaki kwalliyar hauka idan kin fita sai kinyi  Aunty kiyi hakuri daga yau na nutsu ba ruwana dashi kuma zan kame kaina insha Allah na maida hankalina gun karatuna nacikawa Abbana burinsa mikewa tayi ta shiga bedroom dinta taje tayi wanka ta canzo kaya ta kwanta saman gado tana juyi tarasa meke damunta har bacci ya dauketa Maheeda har gida ta kawo mata Jakarta da yamma tayi mata godiya sosai taje rakata mai gadi ya hanata yace bakin kofar get bazata bakin titi ba Dole ta hakura ta tsaya daga kofar get sukayi sallama ta hango wasu mutane suna nuno gidan amma ganin gidaje ukkune jere yasa juya ta koma cikin bata Jima da zamaba mai koya mata turanci yazo ya koya mata sai dab da magrib ya tafi taje tayi sallah Dan shida kansa yayi mamakin yada yau ta nutsu tayi karatu niko nace hammm ai dole
Misalin 1100pm na dare zaune yake da farin gilashi manne kan fuskarshi Laptop gabansa yana dannawa sai murmushi yake Saki tana zaune kusansa  my man shiru bai amsaba saboda hankalinsa Akan abinda yake dubawa kana ganinsa afarin cikin yake jikinsa ta kwanto ta cire gilashin idonsa tana kallonsa my man nawan jimana meye yatafinmin da hankalinka haka murmushi yai ya tsayar da abunda yake ya Kara janyota jikinsa cikin amon muryasa mai zaki yai kasa da murya ya Dora bakinsa saman kunnetamy bintuna ya akayi ko rigimarce ta motso  rumgumesa tayi tana dariya  shafar kitson kanta yai suna kallon junansu suna murmushi kiss ya sakarmata saman lips dinta  my man nawan gira ya daga mata sakone yashigo cikin wayarsa kafin ya dauki wayar kira yashigo yana rungume da ita ya dauki wayar yai picking ya Kara akunnesa hello yes gud hakan yayi ina godiya babu adadi daganan ya tsinke kiran


 wata wayar ta sake daukan ruri ya kalli screen din wayar ganin mai kiran cikin rawar jiki ya dauki wayar yayi picking  Aslam hajiyarmu Allah yakara miki lafiya da tsawon rai kome tace yayi dariya niko nace Dama yana dariya Yajima yana magana yaba bintu ta amsa cikin girmamawa tana gisheta  hajiyarmu wlh duk sunyi bacci gobe akwai school ne eh har Rudat tayi bacci yanzu ta gamamun rigima tayi bacci hannusa ya zura cikin rigarta yana lalubarta da sunsunata duk ta dabarbarce Dole ta matsa daga jikinsa tayi nesa dashi tana amsa wayar shiko murmushi yayi ya cigaba da abinda yake a Laptop sai murmushi yakeyi tajima suna hira da surukartata mai dattaku sukayi sallama ta ba man dinta sukaci gaba da hirasu sun Jima kafin suyi sallama ya kalli bintu  my tauraruwar zuciyata bacci nakeji kinsan fah gobe inada tafi ya fada yana kashe Laptop ya Mike tsaye ya ware mata hannayansa kafada ta makale Allah my man sai ka daukeni matsawa yai kusanta ya sunkuya ya ciccibi abarsa tana dariya ta rikeshi gama bedroom dinsa ya nufa da ita  my bintuna kinfiye wayo wlh kiss ta masa awuya  to my man menayi kuma shiru yamata yana murmushi kan gado ya direta  ko zakimun wanka   my man nide jekayi kazo bathroom ya shige ya jima kadan kafin ya fito daure da towel yana goge jikinsa Window ya daga yana leken harabar gidan ko ina ya wadatu da haske jamian tsaro ta ko ina sai shawagi sukeyi kai ya girgiza gun CC Tv camera yaje yana dubawa haka wajan gidanma ko ina da matakan tsaro kai ya


 jinjina agaguce ya shirya ya saka jallabiya ya tayar da sallah rakaa biyu yayi Yajima yana Addua muryashi can kasa  yake magana  my noor Dina Allah ya Kara daga haskenki a fadin duniya zan kasance mai farin ciki idan haka ta kasance   muryasa ta Kara yin kasa  banji me yaceba Yajima sosai kafin ya tashi ya cire jallabiyar yasaka kayan bacci ya fesa turare mai masifar dadi ya haye gado ya kwanta ya kashe wutar dakin duhu ya baiyyana  my bintuna kinyi bacci shirun da yajine yagane ita kam akwai saurin bacci rumgumeta yayi gam jikinsa ya tura harshensa kunneta sai ta kyalkyale da dariya  my man ka bari shiru bai cemata komaiba ya shiga sauya mata lisafi cikin zazafar soyayyarta soka fara farantawa junansu rai Asubah ta gari bintu Aliyu 
Bayan shekara biyu

Rayuwa kenan yau da gobe mai maida yaro babba rayu taja sosai yau Aliyu Mohammed Damba ya cika shekaru biyu kan mulki Wanda abun Alkhairin da yayiwa garinsa da jaharsa ya baxa ko ina kullum kimarsa karuwa takeyi aidanun duniya farin jininsa kullum gaba yakeyi kyatu da sadaka ta zame masa jiki da temakon nakasassu shiyasa abokan gaba suka tisasa gaba Wanda basusun kasa taci gaba


Amma haryau Allah bai basu saar cin galaba akansaba Teemah tun abinda ya faru ta fita harakar gwamna ta rufe babinsa arayuwarta saide sonsa na manne cikin zuciyarta ta binne tunda ta gane babu wani Faidar yin hankan ta maida hankali wajan karatunta yanzu ta shiga JSS 3 masha Allah ta goge ta zama cikakuyar budurwa kyawunta ya fito ta murmure kirjinta ya ciko saide bata fiye manyan breast ba kuma ba kananu baneba tsaka tsakiya suke wlh idan ka ganta akacema abaya tayi wannan shegiyar kwalliya zakasha mamaki ta nutsu yanzu bata fiye hayaniya ba idan ba tana tare da Maheeda ba ko malika Abu biyu ke damunta ayanzu irin daga masu sayar da ruwan jarka abaro sai mahauta masu nama ko yan yawan zamana gari banza sun adabeta da soyayya itako Allah yanagani tunda ta rasa gwamna har yau bata taba jin son wani mutumba aranta dan haka take fakewa zuwa gidan gwamna aboy amsar sadaka kawai dan tagansa taji dadi kuma tunda take zuwa cikin ikon Allah shine yake bata da hannusa gun jerin Almajirai amma rufe fuskarta take da hijab mai niqab bayaganin fuskarta bare yasaakorata ko akaita gidan mahaukata tunda take amsar kudin bata taba kashewaba saide tayi ta sunsunawa tanajin kamshinsa tana farin cikin akwai wani mutum mai kudi kwanaki ya matsa mata saida tayi kwana biyu bataje school ba haka zai rika turomata kudade sama da dubu dari da wayoyi masu masifar tsada da kayan ciye ciye bata taba amma saba ita dan tsoronsa matakeyi abun da ya isheta tunda har yanzu bata da waya ta fadawa Malika itako Ta kirayi Muazzam ta fada masa yana cikin aiki ya bari yazo dan yaji tsoron yada sukace yana bata makudan kudi bata amsa


Tsoro yake a yaudari yar mutane da yaje ya dauko amana da rana tsaka yazo cikin saakuwa ya hadu da mutumin yace yana sontane da aure da aka tuntubeta tace bataso ya shafa mata lafiya karatu zatayi Dole ya rabu da ita amma sai me kullum duk inda zata ko makaranta ko islamiyya sai taga wata jibgegiyar mota na binta ko taganta jikin gidansu to abin ya dameta amma baa taba mata magana ba sai dai tana ganin masu motar su biyune har cikin makarantar suke shiga suna zagaye amma babu Wanda ya taba musu magana ta fadawa Malika tace kawai itace take ganin binta sukeyi harakarsu daban tafita bayansu shine tayi watsi dasu ko suna binsu abaya idan direbanta zai kaita makaranta ta fasa damuwa tunda Malika tace ba itaba sukebi hakade rayuwar ke tafi masha Allah teema akwai farin jinin har masu shayi da birediMisalin karfe Shida na yamma ta fito daga islamiyya cikin Nutsuwa take tafiya da sauri sauri saboda hadirin da ya gangamu ga iska duk atsorace take saboda motar na biye da ita wata yar kwana Ta karya sukaci karo da dantani mai ruwa ya turo baro ya washe baki  ah Fadima daga ina kiyi sauri kar afara ruwa fuska ta kwakwabe  dan Allah meyasa kuke takuramun me na tsare mukune ruwan da ya fara zubowane yasa bata ida maganar ba dantani ya saki baron ruwan tana tafiya ya bita da gudu  muje na rakaki karki jike zazzzabi ya kamaki na shiga uku dan kudin auran da nake tara mana ya kare amagani hannusa ya beka zai rike mata hannu yaji shi akasa a shmfida wani murdeden mutum yamasa bugu daya atake ya suma ihu ta kwara ta gigice ta rasa hanyar bi mutumin daya ya daga dantani ya sauye masa robar ruwa ya farfado ai da gudu yayi gun baronsa tana cikin gudu mota ta sha gabanta Dole ta tsaya tana zaro idanu motar da take biye da ita kullum ta tsaya dab da ita wannan Wanda ya sumar da dan tani ya fito yana zaro mata idanu  ke maza shiga wannan motar duk da tana tsoro amma ta dake cikin dauriya tace naki bana shiga ku kasheni idan kasheni zakuyi me na mukune wai bindiga taga ya zaro ga uban ruwan da akeyi jitayi fitsari nason kwace mata ta faraja baya yana binta har taje jikinta motor da yakeso tashiga arashin sani Ashe murfin abude kawai sai ji tayi tayi luuuu zata fadi taji an tarota anjanyo an shigar da ita motar daga waje aka rufo motar saman kujera aka zaunar da ita jikinta na tsiyaya ruwa harda dan guntun fitasrinna iya tsorata ta tsorata  jikinta kerrrma yake daket na bude baki zan kurma ihu naji wani tattausan hannu ya rufe mun bakina  akaja motar guje


To fah wanene wannan mai kasadar daukar watsime

Rahma ce ummu Fareesa


MATAR

GWAMNA
    ___________________________________KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

United we stand and succeedOur ambition is to entertain  motivate the mind of readers

httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation

___________________________________


Written By

 Real Ladingo

Yar mutan Niger
Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janafwannan shafin Sadaukarwa gareku comments dinku na burgeni sosai My umaimah Aliyu my ummiee zaria my Shafancy mum Sayyeed malamata my Aishana ummu Nabeel mmn Teemah Nafeesat mareega mmn nanah Firdausi Naimcy my Hadeeza kawata my khadija Saarbukar Rabiu Fadilatu salihu mmn Wasila maryam habibu my Aisha idris duk wannan shafin nakune malakinkune sai kunso akaranta kuji dadinku kuna manne cikin zuciyata i love you lodi lodi
Bismillahir Rahamanir RaheemPage 4wani daddadan kamshine acikin tafin hannusa da ya rufemun baki ya baibaiyeni hannun taushi tamkar na jarirai Wanda yasa nakusa manta da satoni akayi cikin dauriya na  gantsara masa cizo atafin hannusa amma ko gezo bai ba saima wani sansanyan murmushi naji an sakarmu Kara cizonsa nayi akaro na biyu amma baiyi ko gezauba jin taushin hannu ya tsoratani karfa jini ya fito amma tuna satoni akayi cikin Kara harzuka na Dora hannuna kan nashi ina kuka na Kara masa wani uban cizo saida fata ta tashi wata zazakar murya naji yace Ashhhh my Teemah kinjimun ciwo ko bakisan hakori dafi bane da Sauri na dago kai na kalleshi wani haddadan mutumne mai kamala manyan kayane jikinsa farin jajir dashi ingarman namiji gabana naji ya yanke ya fadi Dan zatona wannan mutumin ne yasa aka satoni to bashibane wannan ban sanshi ba tsoro ya Kara kami jikina na rawa ga sanyin da nakeji ruwa sai digo yake ajikina ganin tana rawar saniya tausayinta ya kamashi gefensa ya duba ya dauko wata jibgegiyar rigar sanyi mai masifar kyau bai tsaya wata wataba ya fuskanceta ya zai saka mata ta kiya ta buge hannusa face ya hade tam ba wasa a kaushashe yace ke tsaya na saka miki banson raini ko bakiga yada kike rawar sanyiba ganin yada ya tsare gida yasa na tsaya ya sakamun rigar saman jikeken hijab Dina hannusa Wanda na jiza har nafitar masa da fata na kalla murmushi ya saki Oya kiciza ko kin gaji ne harara na zabga masa duk atsorace nake bansan inda zai kainiba kuma da ganinsa ba karamin mutim baneba tsayar da kukan nayi ina zubar da hawaye Dan tunda ya shigar dani motar ban daina kukaba nace


 Dan girman Allah mai nayi makane meye hadina dakai da kasa aka satuni ina zaka kai dama kaine kake bibiyar rayuwata ka adabeni tunda na fara magana ya zubamun idanusa masu kamar zaiyi bacci tsadaddan murmushi dauke kan fuskarsa wannan mutum da ganinsa akwai jiji da kai abinda ya Kara harzukani ina magana yanamun dariya cikin jin haushin dariya najanyo gefen hijabina Wanda ya Dora min rigar sanyinsa asama yana tsiyayar da ruwa na lafta mishi ajikin sai dukansa nake raina ya gama baci Dan ko ina yarinya babu abinda na tsana in ma mutum magana yana dariya tsayar da dariyar yayi saboda ruwan hijabin duk ya bata mishi fuska rike hannuwana yayi  yi hakuri my Teemah na daina wai Ashe fitinar na nan zansha fama jin dadin muryasa yasa na daina dukansa Dan yanzu cikin wani irin salo yayi maganar Jin na daina dukansa  ya Sakar mun hannuna yana goge 


ruwan fuskarsa nayi mamakin yada baiji tsantsanin ruwan da na yarfa masa afuskarsa ba motar naji ta tsaya dagowar da nake na ganmu kofar gidanmu cikin farin na rinka kiciniyar  bude motar na kasa juyowa nayi na kwakwabe fuska  ni budemun mota na futa barayin yara ta Allah ba takuba wlh ina shiga gida zan fadawa Addata ta fadawa yayana sai an bincikoku duk dariya ta kamasa ya gintse ya hade face My Teemah zo zauna zamuyi magana ta fahimta ganim yada ya sauya lokaci daya yasa ta Kara tsorata amma ta dake saboda bata fiye ma babba rashin kunya ba ta dawo ta zauna wani kwali naga ya janyo ya bata  amshi wannan wayace zan rika kiranki muna hira tsarinki yana burgeni inaso muyi abota dake najima a gombe sunana Aminullah Mujaheed mai jamaa Nine babban duk wani Dan sanda dake cikin garin gombe yanzu shekara biyu kenan ina ganinki duk tsaron da ake baki nine nasaka saboda kina burgeni ko wannan mutumin da ya takuraki nine nan na masa kashedin ya barki tunda bakison sa yanzu insha Allah zan tsaya miki har sai kinsamu wanda kikes o abinda nakeso dake yanzu inaso ki maida hankali gun karatunki kinga kin kusa sauranku wata ukku ku karasa secondary school so kiyi qokari kuma duk Wanda ya nemi zai takura ki fadamun amshi wayar  fuska na yamutsa duk da muryasa namun azabar dadi duk ta kashemun jikina amma na dake nace  banaso ka barshi ni bana amsar abin mutum kuma banayin qawance da namiji ina ka taba jin hakan ka fadi gaskiya kawai kace kanason cutar dani sai na sakankance ka yaudareni to bari kaji karka ganni yar karama kamar kurciya ka daukeni jahila inada ilimin Addini da boko dan haka aje anemi wata ayaudara ba niba naki banason wayar karike abinka karka kara nuna ka sanin ko ahanya kuma sai na fada agida 


murmushi ya saki kafin ya hade fuska tam ya kamo hannuta ya dora mata kwalin wayar ya saka idanusa cikin kwayar idanunta jikinta ya saki ta farajin kasala dan idanusa tamkar wani sinadari na kawayar bacci ne acikinsa kanta ta sada  kinsa Allah my Teema idan baki amshi wayarnan ba sai nayi mugun baki mamaki ga in da ake son ceto rayuwarki kinacan kina fama da son Wanda baima san kinayiba to wlh idan baki amasaba sai nasaka ancutar da mai girma governor sai na wulakantashi sabode ke dan munsan komai shine kike so  baki kola kowane namiji da sauri na kallesa idanuna suna zubar da hawaye na rike wayar na rungumeta kirjina  kayi hakuri Aminullahi wlh zan rike wayar koda yaushe ka kirani zan dauka karka cutarmun dashi ina sonsa har nabar duniya amma bazai taba saniba saboda ya tozartani yacimun mutumci yasa ankaini gidan mahaukata Allah ne yasoni yanzu da inda takardar hauka abin


Na batamun rai amma kuma sonsa ajinina yake babu Wanda ya isa yasa na fasa sonsa kayi hakuri karka cutar dashi please  ok kina nufin bazaki kula kowani namiji haka zakiyi tazama saboda shirmen ki  ni banceba yanzu dai mubar maganar badai waya bace kawai kake bukata muyi da abuta naji na yarda mutuikar bazaka cutarmun da My Haidar ba  tsaki yaja  karki karmun zancansa mutikar bani namiki  inada kishi ki kiyaye wannan abunda kikeyi zai saka na kara tsanar governor wani har nacutar dashi kuka ta fara ta riko hannusa  don Allah karka cutar dashi naji idan dai bazaka saka acutar dashiba wlh naji bazan kara sonsa ba zan yakiceshi azuciyata har Allah ya bani wani kaji Aminullahi miskilin murmushi ya saki kafin ya hade face  ok naji amma da sharadi  da sauri nace naji fadi sharadin  karki kuskura ki nunawa wani wayar ko kifadawa yayarki  ko iyayan mijin yayarki ko kawarki maheeda kuma inaso ki cireshi aranki mutikar kikayi haka to bazan cutar dashiba zabi ya rage naki tunani nayi naga so azuci yake ba gani zayiba nafasa ko ban fasaba  OK na yarda duk zanyi abinda kace kaima kuma kasa adaina bibiyata tunda ga waya shiru yamata miskilacin ya motsa bai sake magana ba yabeka hannnu ya bude mata mota bata jira komaiba ta fice da gudu ta nufi ciki kai ya girgiza yana sakin murmushi direba yaja motar suka tafi wayarsa ta dau ringing bai dagaba ya dauki wata ya danna wata number buga daya aka dauka murmushi yasaki yace aiki na kyau da alama buri zai ciki Dan naga alamun nasara kitt ya tsinke kiran wayoyi har biyu suna ringing yaki dagawa tsaki yaja ya lumshe idanusa yana shafa sumar kansa mai yalwar gashi yana tuna ta inda zai fara Dan yasan da yarinyar burinsa zai cika murmushi kwance kan kyakyawar fuskarshi idanusa ya bude ya kalli gun da ta zauna duk lemace ta ruwan da ya jikata tsaki yaja yana Kara matsawa nace daga baya kenan malam Aminullahi ka manta kaine ka dauketa cak ka zaunar da  ita a motar kuma har ruwan saida ta gogama afuska 
ko da ta shiga gida duk arikice take ta tsorata da wannan kyakyawan mutumin mai cike kwarjini kwalin wayar ta boye ajikinta bata tsaya parlo ba ta shige bedroom dinta ta boye wayar tacire rigarsa tana sunsunawa ta ajiyeta bakin gado ta cire jikakun kayanta ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro Alwalla ta fito tasaka doguwar Riga Maras yauni ta fito parlo kenan taji kiran sallah magarib malika na zaune tana shayar da yarta ta kalletaFatima ina kika tsaya har ruwa ya jikaki haka naga ficewarki ko kallonmu bakiyiba  zama tayi ta Dora kanta kafadar malika  ban tsaya ko inaba Aunty lokacin da na fito aka fara ruwan kallonta tayi taga kamar da damu aranta cire yar tayi daga shayarwar ta kwantar da ita gefenta ta rumgumo Teemah tana buga bayanta  ki fadamun damuwarki ko kinada wacce zaki fadawa murmushi ta kakalo wlh Aunty ba komai kawai dan dai ruwa ya jikanine sanyine nakeji fah ta fadi tana dariya ajiyar zuciya  ta sabke wlh har naji dadi nazata ko wannan mutanan da kikace suna binkine suka tareki amma rigar waye ajikinki mai shegen kyau daganinta ba takarmun mutumba daga ina kika samu gabanta yayi mugun faduwa tsoranta ya baiyyana cikin in ina tace Aunty da Ma Malam neYabani wai nasaka tunda gidan da dan nisa kar ruwa ya jikani  amma Allah ya saka masa da Alkhairi shikuwa  ina  yasami irin wannan Riga mai tsada maganar na basar na saketa Aunty muyi sallah dariya tayi  wlh kisan na dan rudene nazata cikin damuwa kike yayanki ya kira yace agaisheki yananan tafe cikin satinan murna sosai nayi  Allah ya kawoshi lafiya bari nayi sallah nazo ki kiramun shi mu gaisa jiya banji muryashi ba na fada ina shiga bedroom dina  sallah nayi ban tashiba saida aka kira isha nayi 


najima ina Addua Allah ya kare gwamna kar kyakyawan mutuminan ya cutar dashi akaina mikewa nayi Dana tuna kashedin da yamun mutikar ban kunna wayarba zuwa nayi na daukota na cirota daga kwalinta naga iPhone ce kuma karshan kudin jikinane ya dauki rawa  wlh bazan kunna wayar nan mai uban kudiba ba ruwana dan naga ta hannu yaya Muazzam bata kai kudin rabin wannan ba jikina na rawa na maida wayar kwali na boyeta naji Malika na kirana nutsuwata na saita dan ni yanzu nafi tunanin kyakyawa dan yankan kaine dan natuna kusan inda na zauna dauri dauri uban kudin da nagani fitowa nayi har ta hado mana abunci saman carpet muka zauna bamu je kan dining ba Rasheeda na saman cinyata ina bashi munaci muna hira da Aunty har muka gama ta kirawo yaya Muazzam tabani mukasha hira yana tambayata da matsala ko wani mai takurani nace babu munjima sosai muna hira  kafin muyi sallama  yau munjima sosai muna hira da Aunty kafin naji barci Rahseed yace yau gurina zai kwana najashi muka tafi  kwance nake sai juyi nakeyi tunanin ya zanyi na cire son gwamna azuciyata dan kar mai kyau ya cutar dashi jinayi ko zaa rabani da raina bazan iyaba amma zanyi kokarin dannewa sadakarma zan daina zuwa amsa sai jifa jifa dan kar aje ya gano yasa acutarmun da gwamna Adduar bacci nayi na rungume rigar mai kyau saboda kamshinsa yayi shige da na My Haidar duk akwai banbbanci amma sai nasaka akamshin My Haidar dan nasami bacci mai dadi bajimawa bacci ya dauketa asubah ta tari .


Karanta: Matan Asokoro Hausa Novel Complete

Post a Comment

0 Comments

Close Menu