Karshen Wahala Hausa Novel Complete

Ad Code

Karshen Wahala Hausa Novel Complete

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin Karshen Wahala Hausa Novel Complete.

Karshen Wahala Hausa Novel Complete

K'ARSHEN WAHALA


Episode (41)Satin su d'aya da dawo wa abuja abduljabbar ya shirya musu tafiya honey moon shi da nauwara twins wajen aunty asma'u suka ajiye su saboda makaranta, hutun 2 month's ya samu don hka suka d'aga xuwa k'asar Greece daman k'asa uku xasu Greece, switzerland, sai su biyo ta Saudi Arabia suyi umarah. 

Sun sauka a k'asar Greece k'asa ce mai kyau sosai da mutanen mu na Africa basu saba da xuwan ta sosai ba a wani babban hotel yayi musu masauki suna hawa na uku, room d'in da suke ciki katon parlour ne da one bedroom shima babba sai toilet, nan suka xube kan bed suna huta gajiyar mikakkiyar tafiyar da suka yi. 

Bayan sunyi wanka sun ci abinci sannan suka kirawo su umma suna sanar dasu sun sauka lafia, sun kirawo aunty asma'u ta had'a su da twins suna ta xuba musu surutu kowanne yana fad'in tsarabar da xa'a yi mishi, sai da suka yi k'wanaki uku suna hutawa basa xuwa ko'ina suna manne da junan su ana xuba soyayya don abduljabbar yace ta shirya Insha Allah xai sun dawo da tsarabar honey moon ya kuma dage da addu'a sosai. 

A k'wanakin su na hud'u da xuwa k'asar Greece ne da wani yammaci bayan anyi ruwa an d'auke suka fito abduljabbar yana sanye da white d'in trouser nd T-shirt red colour ya d'ora jibgegiyar rigar sanyi black saboda yanda garin ya d'auki sanyi sosai, yayin da nauwara ta sanya dogon wando maroon colour nd T-shirt black sai ta d'ora coat irin wanda mata suke sanya wa har xuwa gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da maroon veil tayi kyau sosai suna rik'e da hannun junan su suna tafiya. 

Sunyi yawo sosai a k'asar Greece di'n nauwara k'asar ta birge ta a sati ukun da xasu yi sun sha yawo duk wani gurin shak'atawa da manya manyan malls na k'asar sun xiyar ci wajen da hka suka yi bankwana da k'asar Greece suka yo switzerland nauwara tana santin k'asar don ta matuk'ar yi mata kyau. 

Bayan sun sauka a k'asar switzerland ne da sati biyun nauwara ta fara jin canjin yanayi a tattare da ita yawan bacci da rashin appitate a baki sai kuma tashin xuciya kamar yau ta gama shirin ta xasu fita da abduljabbar tana jiran shi ya fito daga wanka irin ta xauna jiran nan shi sai bacci yayi awon gaba da ita a hka ya fito daga toilet d'in ya tsaya kallon ta cike da mamaki wannan baccin na nauwara yana d'aure mishi kai sosai mybe fitar da kuke shi yake gajiyar da ita Cewar wata xuciyar tashi gaban dressing mirror ya K'arasa ya gyara jikin shi ya K'arasa inda take tana bacci a hankali yake tashin ta bud'e idon tayi yana kallon ta yace 

"baby nah ko mun fasa fitar ne,  ni wannan baccin naki na lafia ne anya babu ajiya ta Anan???? "

Yatsine fuska tayi ta bud'e baki xatayi magana wani amai ya taso mata da gudu ta nufi toilet ta dunga k'wara shi sai da ta amayar da duk abin da taci, yana rik'e da ita kamar xai fashe da kuka haka yake ji don ba k'aramin tausayi ta bashi ba ganin yanda take wahala kamar ba soja ba bayan ta gama ya sake mata wanka sannan suka fito xuwa daga toilet d'in ya sa mata kaya tukunna yace 
"taso mu tafi hospital ni nagaji da wannan yanayin da kike ciki baxan iya jure ganin Kina ciwo ba"
Cikin shagwa6a tace "ni gaskia a'a xan samu sauk'i bana son ayi min allura "
Kamo ta yayi tare da mik'ar da ita tsaye yace "baxai yiwu ba dole ne muje a duba min ke don nasan me yake damun ki "

Ba don taso ba ta bishi suka je wani hospital sun samu nasarar ganin wani Doctor mai jan kunne yayi mata en tambayoyi sannan aka yi mata urine test Inda suka hango d'an k'aramin ciki a manne a jikin ta lokacin da suka sanar da abduljabbar nan take ya tsugunna tare da yin sujjadar godiya ga Allah yana tashi daga sujjadar don tsanani murna ya rungume doctor d'in Kafin ya jiyo kan na ya d'auke ta cak sai juyi yake da ita a office d'in Dr di'n ya bisu da kallo alamar sun burge shi sosai daman en 9ja sun iya soyayya da kula da matan su kamar yanda ya gani a Wajen abduljabbar, Cewar Dr a xuciyar shi bai san maganar ta fito fili ba har naji ina da gefe na ce lallai doctor nan an gaya maka en 9ja basu da wannan wayewar nan me ka dau ke su ne 😏, muma ae mun iya kawai dai don malam bahaushe akwai shi da son girma baya son rai ni shi yasa ba kowanne yake yi ba..... lol 
Jin abin da na fad'a yasa doctor ya sunkuyar da kae yana sosa k'eya alamar yaji  kunya bai san xan ji ba lol. 

Bayan ya gama juyin da ita a office d'in doctor ya dire ta sannan a lokacin Dr yayi wa abduljabbar bayanin yanda xasu kula da cikin Sannan ya rubuta mata magungunan da xata sha wanda xai taimaka mata sosai wajen Inganta lafiar ta da ta jaririn cikin. 

Da hka suka yi sallama da doctor suka fito xuciyoyin su cike da tarin farinciki more especially abduljabbar da hka suka tari taxi har xuwa masaukin su. 

Nauwara ta ga gata sosai a wajen abduljabbar wanda Idan yana wani abin har mamaki yake bata kamar bashi da wasu yaran, shi haka Allah yayi shi akwai son yara sosai, nan da nan nauwara ta dad'a wani irin haske kyanta ya k'ara fito wa sai dai ta d'an rame saboda laulayi yau lafia gobe sai a hankali, satin ukun da suka yi niyyar yi sai da suka k'ara Sati d'aya sannan suka wuce Saudi Arabia nan ma Sati ukun suka yi sannan suka yo gida nigeria,  sun sauka lafia aunty asma'u ce da su twins sai yaranta sune suka xo taryar su cikin tsananin farinciki na'eem da ameer suka rungume iyayen nasu suna murnar ganin su don sunyi matuk'ar kewar su, kallo d'aya aunty asma'u tayi wa nauwara ta fahimci ciki ne da ita don hka cikin murmishin tsokana ta cewa abduljabbar
"kai daga xuwa honey moon sai ku dawo da tsaraba"
Cikin murmishi yace "alamar tafiya tayi kyau sosai "
Yana fad'in hka ya shige mota kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa aunty asma'u kuwa dariya tayi tana cewa "Allah ya shirya ka abdul "
Da haka suna er hirar su suka K'arasa gidan nasu sai yamma likis aunty asma'u ta koma gidan ta ta bar mata babbar 'yarta hanan Ko xata taimaka mata hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayi wa nauwara ba don jinin su ya had'u da hanan yarinyar akwai hankali da kamun kai. 

Sai da suka yi wajen wata biyu da dawo wa sannan abduljabbar ya samu d'an short break na tsayin 1week kacal suka tattara suka yo kano don tuntuni nauwara taso xuwa but ya hana ta sam yace tare xasu xo don baxai iya missing di'n ta ba na tsawon wasu k'wanaki, lokacin cikin jikin ta har ya dan fito ana ganin shi. 

Sun sauka a Kano lafia umma,abba, aunty sadiya da ammi ba k'aramin jin dad'in ganin su suka yi ba gashi sun hango Sun kusa samu wasu jikokin nan fa suka frasa inda xasu sa su don dad'i, abin da yayi matuk'ar d'aure kan nauwara shine ganin wai ammin ta da ciki gashi nan ya fito ana ganin shi lallai wani baya haifar d'an wani rayuwa kenan Allah yasa mu dace da kyakkyawan rabo. 

Washe gari fa'iza ,jiddah aunty kausar taxo gidan gaba d'aya kamar had'in baki sun sha murnar ganin junan su fa'iza ma tana d'auke da cikin ita ma jiddah Allah maji rokan bawan shi gashi nan ita ma da nata cikin kuma yanxu hindatu tayi nadama tun lokacin da aminu Yayi mata saki d'aya da tayi niyyar k'ona jiddah da tafassheshen ruwan xafi Allah bai bata nasara ba aminu ya ganta ya kar6e to shine yayi mata saki d'aya, dakyar ya dawo da ita don darajar yaran dake tsakanin su, yanxu tayi nadama sosae xaman lafia suke da jiddah ae duk tsanani yana tare da sauk'i komai wuya sai dad'i kuma *Innallaha ma'assabirin* littafin miss zahra mansur. 

Yini guda suna shan hira nauwara kowanne ta bashi tsarabar shi sun yi mata godia sai yamma tukunna kowacce mijin ta yaxo ya dauke ta. 

Satin su d'aya a Kano sun xagaya gidajen en uwa har kaduna nauwara taje k'wanan ta d'aya ta dawo kano, ranar sunday suka shige abuja saboda makarantar su na'eem da ameer, yanxu saleem ya had'a degree di'n shi akan harkar kasuwanci bai nemi aiki ba Abba ya wulla shi company nin su nauwara dake abuja don ya dunga kula shi ya had'a shi da kwararrun ma'aikata masu tsoron Allah da amana a xuciyoyin su nan da nan company nin ya fara samun cigaba yanxu saleem ganin shi sai week end a Kano sauran k'wanaki biyar di'n a kaduna tun an fara  xama babban mutum yanxu aure ya rage mishi don duk wani jin dad'i ya same shi, ammi kullum cikin addu'a take ma yaranta dasu umma da abba da suka rik'e su tsakani da Allah.... 

.

Gaisuwata ta Musamman Ga Qanwata Wato:- Ummulkhairi Muhammad Kabir tare da Fatan kasancewarki cikin qoshin Lafiya.

Mutane da dama Suna ta tambayata Wai Yaya akayi Ni Banyi Aure ba Amman Kuma 'Yata Ummusalma Sadeeq  ita Kuma zatayi? Wai Daman hakan na faruwa? Ace Uba bayyi aureba Amman Kuma gashi har 'Yarshi zatayi? To masu yimin wannan tambayar Babu abinda Zance muku saidai kuju tsoron Allah Ku daina Yawan bincike! Wannan lamari Bai shafeku ba, don haka ku Fita daga idona na rufe!

Wala Ta Jassasuuuuu......


Page Daya Kawai ya rage Mana mu kammala wannan Littafi...........

Post a Comment

0 Comments

Close Menu